Mutuwar Janar Idris Alkali Abin Dubawane

Test Footer

Mutuwar Janar Idris Alkali Abin Dubawane




DUNIYA TA SAN DA WANNAN!

Daga Datti Assalafy

Haka kawai ‘yan ta’addan berom ba zasu tare motar Janar Idris Alkali bayan ya fada musu cewa shi babban hafshin soji ne mai mukamin Janar amma basuji tsoro ba suka kamashi suka kashe, dole akwai wani abu wanda binciken kwakwaf ne kadai zai bayyana, domin mun samu bayanai daga wajen ‘yan uwanshi na jini cewa Janar Idris ya bada wasu shawarwari kwanakin da basu wuce biyu ba sai wannan abin ya faru da shi.

Hakika ‘yan ta’addan berom sun taba zuciyarmu, sun yiwa ‘dan uwanmu musulmi mafi munin wulakancin kisa, ku kashe mutum ko bunne sannan ku sake tonewa ku jefa a rijiya, wani irin wulakanci ne wannan?
Jama’a zaku iya tuna wani screen short da na daura muku kwanakin baya?, inda wani ‘dan ta’addan berom ya tabbatar mana da cewa Janar Idris Alkali ya mutu, kuma mutuwar wulakanci, idan kun tuna na saka muku har da hotonshi.

Rundinar sojin Nigeria tace bayan sun jefa gawarshi a rijiya sai suka jefa manyan duwatsu masu nauyin gaske a kan gawarshi, saboda tsabagen wulakanci da kasancersu cikakkun tsinannu bakaken kafurai maguzawa ‘yan ta’adda.

Na saurari jawabin da Birgediya Janar Umar Muhammad yayi bayan sun fito da gawar Janar Idris Alkali daga cikin rijiyar, yana alwashin cewa duk wanda yake da hannu a kisan Janar Idris Alkali komin gatansu da duk wadanda zasu tsaya musu wallahi sai sun fuskanci hukunci.


To abinda kawai za’a mana ya kwantar mana da hankali shine a shafe garin Dura-Du daga tarihi, a rusa garin, a mayar da garin sansanin horar da jami’an tsaron Nigeria, sannan a sakawa sansanin sunan Manjo Janar Idris Alkali domin ya zama abin tunawa har zuwa ranar da Allah (SWT) Zai tashi duniyar.

Jiya babban yayan marigayi Janar Idris Alkali Air Commodore Ibrahim Alkali (Mairitaya) ya bada sanarwan cewa za’a gabatar da sallar “Salatul Ghaa’ib” wa Marigayi Janar Idris Alkali bayan sallar Azahar a babban masallacin juma’a na garin Potiskum dake fadar Masarautar Fika, bayan sun samu tabbaci daga rundinar sojin Nigeria cewa an gano gawarsa, amma kafin lokacin sai aka dage sallar.

Salatul Ghaa’ib wata irin sallar jana’iza ce da ake gabatar wa duk wani musulmi da ya mutu amma ba’a samu gawarsa ba, ko kuma gawarsa na hannun wadanda ba musulmi ba ana iya masa Salatul Ghaa’ib.
Lokacin da Sarkin Habasha Sarki Annajjashi ya rasu, kuma ya rasu a hannun jama’arshi da ba musulmi ba, sai Annabi (SAW) ya gabatar masa da Salatul Ghaa’ib.

Kamar yadda rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwa tace yanzu haka gawar Janar Idris Alkali tana babban asibin shiyya ta uku na rundinar sojin Nigeria dake birnin Jos, ana jiran umarni na gaba daga hedkwatar tsaron sojin Nigeria dake Abuja kafin wani abu ya biyo baya.

A hoto na farko Janar Idris Alkali ne tare da mahaifiyarshi Baaba Halima ‘yar shekara casa’in da uku, itace wacce yafi so da kauna a duniya, ance ko yaje gida hutu baya kwana a gidansa sai a gidansu na gado kuma a dakin mahaifiyasar suke kwana tare yana debe mata kewa yana mata hidima, jama’a kuna tunanin Allah zai kyale mutanen da suka raba irin wannan soyayya da ladabi dake tsakanin uwa da ‘danta? wallahi su kwana da shirin cewa zasuga mummunan sakamako tun daga nan duniya.

Yaa Allah Ka jikan Janar Idris Alkali
Allah Ka sa ya dace da mutuwar shahada Amin.

Post a Comment

0 Comments