ZABEN 2019
Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri'u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya a jam'iyyar APC, tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya ce "babu tantama shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kan kujerarsa a zaben 2019 da izinin Allah.
Mallam Shekarau ya ce zaben da za a yi a badi 2019 ba irin na 2015 bane. Musulmi da Musulmi ne kuma dan arewa ne da dan arewa a tsakanin APC da PDP. Don haka Buhari zai kada Atiku amma ba da irin rinjayen wancan yanayin ba.
Duka wadannan kalamai, Mallam Shekarau ya yi sune a ranar Talatar da ta gabata a garin Badun lokacin da yake zantawa da 'yan jarida, bayan an tashi daga taron kungiyar PSN wato masu harkar magani ta kasa inda suka karrama shi tare da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Ya kara da cewa wannan zaben karo da karo ne, amma Buhari ne mai nasara.
Ana sa rai za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 16 ga Fabrairu 2019, kuma 'yan takara 74 ne za su shiga wannan zabe na shugaban kasa.
0 Comments