*_ZUCIYARMU 'DAYA_ .*
漏Mamuh geee
For you my *zinnie*
_Bismillahir-rahamanir raheem._
1-2
Zaune take Bakin gadon da abbanta ke kwance yana jinya tsawon shekara biyu.
Hawaye ne kwance a fuskarta wa'inda zubowarsu sun zame mata azaliya.
Shekarar abbanta biyu a kwance rigis yana jinya,
Ita ke jinyarsa,ita ke aikin Samar da abibda zasuci duk da qananun shekarunta da basu haura sha bakwai ba.
Kallon 'dakin dasuke ciki tayi
Babu komai aciki banda ru6a66iyar katifar da abbanta yake kai Wanda har gwara tabarma da ita sbd dadewarta dakuma dadewar da abban yayi kwance akanta.
Ginin gidan nasu da 'dakunan gidan gabaki daya sun farfashe alamun ko wane lokaci zasu iya ruguzowa.
Share hawayenta tayi da yagaggiyar atampar jikinta ta miqe zata fita ahankali abbanta yayi magana bataji mai yaceba saita dawo ta zauna tareda kara kunnanta kusa dan taji maiyake fada.
JIDDAH kici gaba dayimin addua Allah ya bayyanamin 'dan uwana kafin nabar duniya.
Sabbin hawaye suka zubo mata tace,
Abbah dan Allah kadaina maganar daddyn lokoja tunda baidawoba kuma kai ba lafiyane dakaiba.
Hawaye yafara yana fadin,
Jiddah inason damqaki a hannun amanane kafin nabar duniya,
Nasani bakida kowa saini,kuma yanda muke dinnan idan na tafi nasan kyararki za'a dinka sbd bakida kowa kuma anai mana kallon almajirai.
Kuka tasaki mai cin rai tana fadin,
Abbah dan Allah kadaka barni tunda Kasan halinda zan shiga idan katafi,
Tun yanxu ana qyamata ana hantarata duk inda naje
Idan katafi bansan yazanyi ba.
Tsit 'dakin yayi sai sheshekar kukanta dake tashi, shima abban nata hawaye yakeyi.
Sundau awa 'daya ahakan kafin ta miqe ta fito tsakar gidansu ta fada 'dakin innarta ta dauko sauran kokon goman data siyowa abban takawo masa ya kurba kadan yace tilas ita ta kurba ko yayane sbd yasan batashaba dan wani lokacin takan kwana biyu ta yini batasha ko taci wani Abu ba sbd basudashi kuma basuda mai basu.
Kofin ta wanke ta jawo kujera ta zauna bakin qofar 'dakin tareda rafka tagumi.
***************
ASALIN LABARI
Ibrahim buba shine cikakken sunan mahaifinta.
Ibrahim marayane datun yana yaro mahaifinsa ya raso sai ya taso dagashi sai mahaifiyarsa inna mero.
Ibrahim yataso cikin gata da kulawa sbd inna mero tana sana'arta ta cikin gida dan haka ta maida duk wani samunta gurin kula da 'danta Ibrahim sbd shikadai gareta har mijinta yarasu.
A makaranta Ibrahim ya hadu da Abdulhameed 'dan dagacin qauyensu.
Sannu ahankali abotarsu tayi nisa sbd halinsu dayazo daya na Neman magana da rashin ji amakaranta.
Abdlhamid shima shi kadai mahaifansa suka haifa,
Mahaifiyarsa ta jima da rasuwa mahaifinsa kawai yarage masa shima babansa yadauki son duniya ya dora masa.
Tsananin son da iyayensu ke nuna musu shiya bada gudunmawa gurin sangarcewa da fara lalacewarsu a qauyen dan tuni suka fara iya tadi da 'yanmata.
Suna ss 2 a secondary Allah ya karbi ran baban Abdulhameed sakamakon guba da aka sanya masa a abinci sbd son kar6e kujerarsa ta mulkin dagacin gari.
Bayan kwana biyu da rasuwarsa aka kuma shirya yanda za'a kashe Abdulhameed Allah yasa yaji cikin dare ya tattara iya dukiyar babansa daya gani ya gudu.
Bugun gida sukaji tsakar dare dama basuyi barciba sbd Abdul yafada musu komai kuma suma kayansu a shirya suke cikin daren suka tattara sukabar garin.
A wani sabon qauye suka yada zango kuma cikin ikon Allah suka samu karbuwa ba 6ata lokaci suka sayi dan gidansu na ginin qasa mai dauke da daki biyu suka tare.
Inna mero ta hadasu ta riqe bazaka taba sanin ba ita ta haifi Abdul ba dan wani lokacinma tafi nuna sonsa akan Ibrahim.
Su kuwa tuni suka qara sangarcewa sbd hatta kayansu innarsu ke wanke musu duk da sun girma.
Ahankali Rayuwa ta canza musu,rashi ya kunno musu kai dan hatta abinci Neman gagararsu yakeyi ga kuma karatunsu yana neman lalacewa.
Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[19:16, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA_ .*
漏Mamuh geee
For you my *xinnie*
_Bismillahir-rahamanir raheem_ .
3-4
Fadi tashi inna mero tafara dan batason karatunsu ya lalace bare taga sunason karatun sosai.
Sanar qosai tafara amma Sam 'dan cinikin bazai yi lalurar makarantarsuba.
Canza Sana'a tayi zuwa ta waina nanma babu wani abin kirki,
Qarshe dai aikin sharar makarantar secondary din dake qauyen tasamu inda duk wata ake bata dubu hudu,
Zuwa tayi ta roqi principal akan ahada kudin aikinta na wata uku riqe abari 'yayanta suyi jarabawa.
Haka kuwa akayi harsuka rubuta jarabawar gama secondary suka dasa wani zaman banxar agida sbd babu abin cigaba da karatun nasu.
Shiryawa inna tayi taje qauyensu dasuka baro ta siyar da 'dan akurkin gidanta tadawo tabawa maqwabcinsu dake aikin photocopy a jami'ar birni yasiyo musu jamb form yacika musu.
Da lokacin jarabawar jamb yayi yatafi dasu birni sukayo suka dawo.
Tunda suka dawo suke shirya yanda zasuyi idan suka fasa birni suka hadu da wayayyun yan mata.
Alhmdullillah sunci jarabawa kuma sun samu admission inda suke karantar law dukkansu.
Sauran kudin gidan sune dama inna ta aje dasu sukayi registration da komai dasuke buqata.
Karatu yayi nisa dan tuni 'yayan inna suka waye suka zama cikakkun gayu sbd sun hadu da abokanai 'yayan masu kudi ga yan mata wayayyu sun samu sbd dama dukkaninsu babu baya agurin kyau irin na asalin Fulani.
Inna tsufa yakawo kai yau ciwo gobe lapia amma Sam batayi qasa a gwiwa gurin 'yan sana'oin dazata tallafawa 'yayanta duk da basuda wata Matsala a makarantar sbd abokanansu dan tuni suka daina zama hostel suna gidan wani Senate dasuke karatu da dansa abokinsu kabeer.
****************
Sun kammala degree dinsu sunyi service kuma cikin ikon Allah baban abokinsu kabeer ya samar musu aiki a cikin garin yola.
Dukkaninsu a kotu suke aiki amma kotu daban daban.
Cikin qanqanin lokaci suka rushe gidansu suka maidashi ginin bulo tareda fidda sashe uku kowannensu daya sbd inna ta matsa akan suyi aure.
Yau juma'a dan haka suna qauyen sunzo sbd dama duk weekend acan suke yinsa tareda innarsu.
Kallonsu innar tayi cikin tsananin kauna da kulawa tace,
Tunda dai nayita cewa ku fidda mata kuyi aure kunqi to nasamo muku matan da kaina.
Ibraheem yayi saurin kallonta zaiyi magana Abdul yarigasa da cewa,
Inna nifa harna samu mata acan kuma ta yarda zatazo ta zauna anan qauye.
Kallon ibraheem tayi tace,
Kaifa nima inna nasamu amma marainiyace batada kowa sai kakarta.
To alhmdllh aiba matsala zanyiwa malam shehu magana saisuje suyo komai.
Wata uku tsakani aka sha biki matansu suka tare qauye gidan innarsu.
Matar Abdul 'yar asalin Sudan ce mamarta ta rasu shine tazo Nigeria gurin babanta arashin sa'arta watanta biyu da zuwa ya rasu gurin kammala takardun gadon babanta anan ta hadu da Abdul harsuka fara soyayya batareda tayi la'akari data fisa dukiya nesa ba kusa ba.
Bayan aurensu kowannensu yasamu cigaba sosai domin kuwa dukiya ta fara zauna musu,
Su inna anje makka ansauke farali.
Fatima matar Abdul ita tafara haihuwa tasamu namiji ibraheem ya nada masa suna TAHEER.
Taheer Nada shekara bakwai Fatima tasake haihu namiji takuma samu wannan karonma ibraheem yayi masa suna ZAID.
har alokacin binta matar ibraheem batada ciki kuma basu daga hankalinsuba sbd ga 'yayanan suna samu daga matar Abdul.
ZAID Nada shekara takwas binta ta haihu ta haifi 'ya mace kyakkyawa.
Sbd murnar haihuwarta harda makka Abdul yaringa biyawa mutane dan ko ibraheem baiyi murnar haihuwar kamar Abdul ba sbd tsananin kaunar dasukewa junansu.
Matayensu har lokacin basusan ba innace uwar Abdul ba.
Sunan inna Abdul yasawa jaririya amma ina tace Sam amaidasa sunan mahaifiyar Abdul data rasu wato MAIJIDDAH.
Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[19:18, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA._*
漏Mamuh geee
For you my *zinnie*
_Bismillahir-rahamanir raheem_
5-6
Tsakanin Jidda da taheer qauna ce sosai dan yana tsananin ji da ita fiyeda komai abinda kawai ke rabasa da ita shine idan zasu makaranta shida ZAID.
Zaid ba ruwansa da Jidda sbd shi haka yataso wani irin miskili dashi ba Jidda kadaiba shi babu ruwansa da kowa kullum yana lafe agurin mamarsa sai kuma inna dan da farko an dauka baida lpia ne saidaga baya aka gano lpiyarsa klau tsabar miskilancine ke cinsa.
Kyawu kuwa tsakanin Jidda,taheer da zaid baka iya tantance wayafi sbd dukkaninsu farare ne hardai zaid daya 'debo fuskar mamarsa Zak shiyasa ma wani zubin ana cewa yafisu kyau.
Taheer ya gama primary zai shiga secondary kenan akayiwa babansu Abdul transfer zuwa lokoja.
Sosai suka shiga damuwar haka saida inna ta basu qwarin gwiwa sosai tukuna suka iya rabuwa Abdul ya kwashi su taheer suka koma lokoja.
Shekara daya a lokoja arzikin Abdul yayi qololuwar buqasa dan tuni yatura taheer da zaid new York gurin karatu tun daga kan secondary.
Ibraheem ma arziki yayi gaba dan tuni ya canza musu ginin gidansu zuwa wani irin mansion dan kowa yanxu 6angarensa sama da qasane.
Da sallah dasu dadyn lokoja yazo (a yadda Jidda ke kiransa)dayazo yaga yanda ibraheem ya gyara musu gida saiyace toshi kuma yadau nauyin zuba komai sabo a gidan.
Qauyensu yayi rai dan kuwa tuni ibraheem da Abdul suka zuba musu titina da futilun sola a ko ina.
Dadyn lokoja yayi komai nashirin tafiyar Jidda new York gurin karatu tareda yayunta inna ta hana tace ita mace ce baxa akaitaba.
Sannu ahankali tun Jidda na tunasu taheer harta manta dasu sbd shekaru dasukaja.
**************
*WATA SABUWA,*
Abdul yakai matakin da aikinsa ya mayardashi qasar Germany.
Yana cikin shirye shiryen tafiya Allah ya karbi ran inna.
Tashin hankalinsu fadarsa zaiyi wuya amma sun shiga matsanancin hali sosai amma ba yanda suka iya sai hakuri.
Rasuwarta da wata 'daya ya wuce Germany cikin alhinin rabuwa da 'dan uwansa, amininsa abokin rayuwarsa.
Hakama su Fatima sunyi alhinin rabuwa da junansu hardai Jidda da Fatima ke masifar sonta.
Isarsu Germany kenan andaukosu daga airport ahanyarsu ta isa gidansu suka samu mummunan hadarin dayayi sanadin ran Fatima nan take shikuma yasamu miyagun raunika da kaririyewa tareda shefewar qwaqwalwa.
Ma'aikatarsu tanan Germany ita tadau nauyin komai nasa bayan sun sanar da 'yayansa dake new york.
Wata 'daya biyu babu waya daga alh Abdul,
Hankalin Ibrahim yayi masifar tashi ga wani tashin hankalin dayake ciki na aikinsa daya rasa saboda mahassada dasuka sakasa gaba.
Kudinsa na banki sunyi qasa sosai gashi babu inna babu abdul.
Lokaci yaja sosai talauci kuwa yayi masa wani irin daurin goro dan takai komai nasa yasaida babu abinda yarage nasa sai gidan dasuke ciki.
Jidda ta zama yanmata tana karatu a makarantar gwamnatin cikin qauyen nasu duk da sai innarta tayi alalan saidawa ake samu aci dakuma kudin lalurar bokonta.
Tanada shekara sha shida ta kammala secondary dinta Wanda tasan babu 'dori daganan sbd babu datayi musu kanta.
Tsanani damuwar rashin sanin inda dan uwansa yake hadi da talauci sun taru sun sakar masa ciwo
Abu kamar wasa saiga ciwo sosai Danko tashi baya iya yi.
A Daren wata talata suna barci tsakar dare gobara takama gidansu sosai
Jama'a sun kawo 'dauki sun fito dasu saidai ana fito dasu Allah yadau ran innarta.
Sun shiga tsananin Rayuwa itada abbanta da tuni ciwo ya qarasa samun guri ajikinsa Danko maganarsa yanxu bata fita said a qyar.
A cikin qonannan gidansu suke rayuwarsu itada abbanta sbd basuda gurin zuwa basuda mai taimaka musu duk da taimakon dasuka ringa yiwa jamaa dasunadashi.
Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:20, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA._*
漏Mamuh geee
For you my *xinnie*
_Bismillahir-rahamanir raheem_
7-8
Rayuwa tayi musu tsanani sbd rashin abinci dakuma ciwon abbanta,ita sutura basama maganarta dan bata ita sukeba.
Aikin wankau tafara yiwa yan qauyen ana biyanta naira biyar a duk kala 'daya.
Da haka take samo musu koko kullum suna sha idankuma tasamu wankin da yawa har da 'dan qosai ko waina take hadowa abbanta dashi, idan kuma batasamu da yawa saidai tabarwa abbanta yasha.
Abbanta bayada zance kullum sai adduar Allah yakawo masa dan uwansa idan har yana Raye.
Takanyi qoqari ta lallashesa idan yafara kukan rashin 'dan uwansa.
Duk lokacin dayayi wannan kukan takanji haushin da tsanar dadyn lokoja da iyalansa naqin waiwayarsu duk da ita bazata iya tuno fuskokinsu ba bare sunayen 'yayansa sbd tun tana yarinya suka rabu.
Shekararsu biyu kenan basuda wata madafa dan tuni tsufa yayiwa abbanta raga raga daga kwancen dan yanxu takai ko tashi baya iyayi yafi shekara akwance.
Jidda farace sosai ada amma wahala,yunwa tareda yunwa sun dafar da ita ta qanjame banda qashi da manyan idanu babu abinda yayi saura a fuskanta.
****************
Sauke taguminta tayi tareda share hawayenta sbd sallamar da akayi.
Wankine aka kawo mata mai uban yawa ta karba babu 6ata lokaci tafara sbd takai abata kudin takarbowa Abba maganin gargajiya gurin mal dauda.
Yini tayi darzar wanki amma bata gamaba sai gab da magariba.
Alwala tayi tayi sallah,duk jikinta ciwo yake sbd wankin harda zannuwan gado.
Ataqaice dai da yunwa suka kwana sbd ba'a bata kudinba sai da safe idan kayan sun bushe takai.
Da daddare ciwon abbanta ya qara tsanani tashi zaune tayi tareda 'Dora kanta kan shimfidarsa ta dingi rusa kuka mai ban tausayi.
Duk duniya babu abinda yakeso sama da 'yarsa tun lokacin data fado duniya,
Dama yana dannewane sbd tsananin son da Abdul yake mata.
Yanaso yarsa tasamu madafa,
Gata mace kuma yarinya dan yanxu shekarunta goma sha takwas.
Ako yaushe hakan kesasa kuka sosai.
Daqyar sukaga safiya tayi
Sallah kawai tayi ta kwashi kayan takai aka bata naira dari.
Gurin mai magani taje daqyar yabata na sittin taje tasiyo kokon ashirin ta rage sauran ashirin dan siyan kokon gobe.
'Daga kansa tayi ta fara basa kokon ahankali amma saitaga kamar baya shiga.
Yawu ta hade dakyar ta kuma basa kunun taga yadawo.
Batasan sanda tayi wurgi da robar kokonba ta girgizasa da qarfi tana kiran sunansa da mugun qarfi.
Abba,abbana, abbana ka bude ido kaji,
Abbana idan kanasona ka bude ido,
Abba nidai kabude ido inason ganinka ahaka.
Abba dan Allah ka tashi.
Idanuwanta sun bushe tsaf ba hawaye sai jajir da idanun sukayi tsabar tashin hankali.
Zabura tayi da qarfi tayi hanyar waje da gudu ko gani batayi.
Karo tayi da mutum a tsakar gidan nasu tayi saurin ja da baya cikin tsoro tareda qurawa fuskarsa ido.
Dattijone fari tas da Hutu ya ratsa fatarsa duk da tsufansa.,
Kamanninsa suka shiga dawo mata tun lokacin tana yarinya.,
Saurin ja da baya tayi tana masa kallon tsana.
Hawayene kwance a fuskarsa suna kwarara shima kallonta yake cikin jin haushin kansa da baqin ciki murya na rawa ya nunata yace,
Wannan ce jiddana?
Jiddata uwata,
Ina Raye jiddana takoma haka.
Wanda yakawosu har cikin gidan yace,
Kwarai kuwa alh wannan Jidda ce.
Share hawayenta tayi cikin dakewar zuciya tace,
Ku su wayene?
Me kuke nema anan?
Kyakkyawan balaraben saurayin dake tsaye tun shigowarsu yana 6ata fuska yace,
Dad inaga fa ba nan bane mutafi tun wata cutar bata kuma kamaka ba acikin wannan gidan.
Ko kallonsa batayiba shi da yayi maganar takalli idris 'dan maqwaftansu daya kawo baqin gidan tace,
Idris ka kaisu gidan dasuke nema dan nan gidan mu bamada kowa aduniya daxai ziyarcemu.
Jiddah kunada kowa,
Kunada gata,
Ni nan nine kowanku kune kowana,
Jiddana nine dadynki, DADYN LOKOJA.
Rintse idanu tayi hawaye suka gangaro mata sbd jin ciwon zancensa.
Tarin abbanta suka jiyo da qarfi.
Juyawa tayi da gudu tayi dakin cikin farin ciki.
Kansa tayi tana fadin,
Abbana bakabarni ba.
Abbana kada ka barni dan Allah.
Ahankali ya bude idanunsa basu sauka ko inaba sai akan dan uwansa abdulhameed.
Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:21, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA._*
漏 *Mamuh geee*
For you my *zinnie*
_Bismillahir-rahamanir raheem_
9-10
Rungumosa dadyn lokoja yayi yaba sakin kuka duk da manyancinsa yana cewa,
Kaicona ni abdulhameed Dana kasa dawowa ga dan uwana harya shiga wannan matsanancin halin,
Arzikina bayada amfani sbd dan uwana jinina da 'yata suna kwana cikin ciwo da yunwa yatashi cikinsu.
Shima abbanta kuka yakeyi yana cewa Allah nagode maka daka cika burina 'daya,
Dayan kuwa koban gani ba nasan dan uwana zai cikashi.
Share masa hawaye yayi yace,
Ibraheem kuka yaqare mana insha Allah tunda muna tareda juna domin na tabbatarda rabuwarmu ba alkhairine agaremuba sbd munga ishara.
Allah kesonmu atare shiya tsaga jininmu da zuciyoyinmu yasaka mana qaunar juna tun muna yara dan haka bazan qara rabuwa dakaiba dan uwana.
Kobayan ranmu nasan zuriar my zasu dorar da wannan qaunar da amincinmu.
Da kansa yasa yasaka 'dan sauran qarfinsa ya dauki 'dan uwansa yayi mota dashi.
Wata babbar private asibiti suka kaisa kai tatsaye aka karbesa tareda basa kyakkawar kulawa.
Babu Wanda yabar qofar dakin acikinsu su uku din,
DADYN LOKOJA, TAHEER DA JIDDAH .
Qarfe uku akace su shiga ya farfado.
Kallon dadyn lokoja yayi tareda kallon Jidda dake raku6e tana kuka yace,
'Dan uwana tunda kabarni banida buri na biyu ne,
Na farko ganinka, na biyu ganin na aurar da Jidda sbd tasamu madafa dakuma gobenta idan babu ni.
Buri daya yacika dan haka koban ga cikar na biyunba nasan kai uba nagari ne ga jiddana.
Nagode sosai dan uwana amma kasani inaji lokacina yayi dazan barka.
Ibraheem bazaka barni sbd banida kowa bayankai,
Inna ta barmu,Fatima ta barmu,binta ma tabarmu Yaya kake tunanin zan rayu idan kaima ka barni.
Kafada min burinka,daya ya cika yanxu insha Allah zancika ma dayan dan yanxu a masallacin asibitin nan zan daur auren taheer da Jidda.
Burina nima danake roqon Allah yacikamin shine Allah ya barmin kai idan kuwa lokacin tafiyar takane yazo ina roqon Allah yadau ranmu atare.
Fita yayi tareda daga wayarsa yakira lauyansa basheer,
Cikin minti biyar sai gashi
Kallonsa yayi yace,
Barr bashir na mallakawa 'yata Jidda Rabin dukiyata.
To kawai Barr yace tareda miqa masa takardu yasaka hannu suka dunguma masallacin asibitin dan daura auren Jidda da taheer.
Cikin rashin fahimta taheer yace,
Dady nifa bangane mai kake nufiba,
Abune mai sauki taheer domin kuwa auranka da Jidda zan daura ayanzun nan kuma idan har nina haifeka kazakace qalaba.
Wani irin mummunan zufane ya tsinke masa sbd masifar datake shirin afka masa gashi dady ya rufe bakinsa.
Abbanta na kwance adakinsa yanaji ta loudspeaker har aka gama daura auren.
Hawayen dadine suka gangaro masa ya kalli Jidda dake raku6e ianuwanta sunyi jajir sbd ita yanxu ko hawayen babu sun Riga sun qafe mata.
Murya asarqe yace,
Jiddana zo kusada abbanki.
A nutse ta matsa ta zauna bakin gadon.
Hannunta ya riqo yace,
Jidda Allah yayi miki albarka keda zuriar dazaki Tara gaba,
Jiddana Allah yabaki hakuri da juriya,
Allah ya hadaki da alkhairai arayuwarki.,
Jiddana kizamo mai juriya da biyayya sbd Rayuwa akwai qalubale atattare da ita.,
Jidda kiyimin alqawarin yin biyayya da jajircewa ki zama 'ya da mata tagari.
Jiddana Allah yazama gatanki ya tsareminke daga mummunar kaddara.
Dago jajayen idanunta tayi takallesa dakyau kafin ta daga kai tace,
Abbana zanyi duk abinda kace har qarshen rayuwata koda kuwa naman jikina za'a riqa diba.
Jiddana....kasa magana yayi sbd kukan tausayin 'yarsa wadda tun yanxu ya hango bushewar zuciya atattare da ita sbd yasan taga Rayuwa amma yasan qalubale na gaba idan ta rasashi.
Allah yabaki ikon jurewa jiddana.
Ameen tace ahankali.
Dadyn lokoja ne yashigo dakin yakalli 'dan uwansa saiyaga yana murmushi.
Matsawa yayi kusa dashi zaiyi magana abban yarigasa da cewa,
Nagode 'dan uwana.
Daga fadar haka kuwa sai Kalmar shahada.
**************
Bugawar zuciyane Yakama dadyn nan take ya zube kan 'dan uwansa yana kiran sunansa kafin shima ya fice hayyacinsa akayi emergency dashi.
Kallon gawar abbanta tayi tareda tofa masa addua batareda tayi kuka ba saidai wani mugun nauyi da zuciyarta tayi mata dan daza'a bude zuciyarta lokacin to dutsi za'aga takoma.
Awa biyu dadyn ya farfado ya buqaci ganin Jidda da Barr bashir.
Cire oxygen din da aka samasa yayi murya na rawa yace,
Bashir ga amanar 'yata,
Kasata makaranta tayi karatu cikin dukiyarta dana bata,.
Jiddana ga bashir nan ki riqesa duk matsakarki ki Sanar masa.
Kallon dadyn tayi cikin tausayin shima rasashi zatayi kenan.
Taheer ya kalla yace,
Taheer ka riqe Jidda tamkar zaid,
Banyafe ku yakice Jidda daga cikinkuba kaida zaid.
Ka lura da zaid da jiddata.
Ka........ Sarqewa muryarsa tayi kafin shahada ta fito daqyar shima yace ga garinku nan.
Sulalewa Jidda tayi qasa a some yayinda Barr yayi kanta da sauri shikuwa taheer kan dadynsa yayi.
*BADA QALA KENAN...*
Mamuh geee馃寱馃寫馃寱馃寫
[21:25, 1/1/2018] 鈥�+234 813 039 8818鈥�: 馃寫馃寱 *_ZUCIYARMU 'DAYA._*
漏Mamuh geee
For you my *zinnie*
_Bismillahir-rahamanir raheem_
0 Comments