Shugaban kasa Buhari ya ce dole wannan kashe-kashen na rashin hankali ya tsaya, musamman a jihar Kaduna da take fama da rikicin kabilanci da na addini, Buhari ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun kamu duk masu hannu a aikata wannan ta’asar ta kisan mutane ba gaira ba dalili, domin su fuskanci shara’a.
Buharin ya furta wadannan kalaman ne a daidai lokacin da ya ziyarci jihar Kaduna don gane wa idon shi irin barnar da rikicin ya yi.
‘Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a wannan rikicin, ba zamu bar masu laifi su dinga walwala ba, don haka duk mai hannu a wannan rikicin ya tabbatar da zai fuskanci hukunci.’ inji Buhari
Buhari ya kara da cewa, ina rokon dukkan al’ummar jihar Kaduna, da su zauna lafiya da juna, ba za mu lamunci tashin hankali ba da kashe-kashe na ba gaira ba dalili, sannan mun yaba da kokarin gwamnatin jihar wajen dakile rikicin.
0 Comments